1 Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.
2 Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku.
3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.
4 Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.
5 Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa.
6 Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.
7 Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.