10 Ubangiji ya ce wa Urushalima,“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,Sarakunansu kuma za su bauta miki.Na hukunta ki da fushina,Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.
11 Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana,Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.
12 Amma al'umman da ba su bauta miki ba,Za a hallakar da su.
13 “Itatuwan fir da irinsuMafi kyau daga jejin Lebanon,Za a kawo su domin a sāke gina ki, ke Urushalima,Domin a ƙawata Haikalina,A darajanta birnina.
14 'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,Su rusuna, su nuna bangirma.Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’
15 “Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba,Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki.Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma,Wurin yin farin ciki har abada abadin.
16 Al'ummai da sarakuna za su lura da keKamar yadda uwa take lura da ɗanta.Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki,Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila ya fanshe ki.