1 Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima,Ba zan yi shiru ba,Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske,Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.
2 Ya Urushalima, al'ummai za su ganki mai gaskiya!Dukan sarakunansu za su ga darajarki.Za a kira ki da sabon suna,Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.
3 Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji,Wato kambin sarauta mai daraja gare shi.
4 Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba,Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.”Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.”Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,”Domin Ubangiji ya ji daɗinki,Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.
5 Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa,Za ku yi murna tare,Kamar murnar amarya da ango.
6 Ya Urushalima, na sa matsara a garukankiBa za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa,Ba kuwa za su bari ya manta ba!