4 Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu.
5 Na yi mamaki sa'ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.
6 Da fushina na tattake dukan sauran al'umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”
7 Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa,Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.
8 Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su
9 daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,
10 amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.