6 Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.
7 Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu'a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.
8 Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,
9 saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai.
10 Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.
11 Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.
12 Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa?