11 Za ku ji daɗin wadatarta,Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.
12 Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al'ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.
13 Zan ta'azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta'azantar da ɗanta.
14 Sa'ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”
15 Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.
16 Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.
17 Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.