6 Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama'a, don su haɗa kai da su, sa'an nan su naɗa ɗan Tabeyel.
7 “Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba.
8 Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.
9 Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya.“Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”
10 Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce,
11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”
12 Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”