4 Kafin yaron ya isa kiran mama ko baba, Sarkin Assuriya zai kwashe dukan dukiyar Dimashƙu da dukan ganimar Samariya.”
5 Ubangiji kuma ya sāke yi mini magana.
6 Ya ce, “Saboda wannan jama'a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka,
7 ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa.
8 Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.”Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar .
9 Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!
10 Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.