18 Muguntar jama'a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.
19 Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko'ina a ƙasar, yana hallakar da jama'a, kowa na ta kansa.
20 A ko'ina a ƙasar jama'a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har 'ya'yansu ma suke ci!
21 Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.