1 Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,
2 “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa.
3 Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa.
4 Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku.