18 Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa'an nan ku sa mutane su yi tsaronsu.
19 Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”
20 Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.
21 Sa'an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra'ilawa.
22 Sa'an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.”
23 Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.
24 Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.