17 tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba'al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su.
18 Joshuwa ya daɗe yana yaƙi da su.
19 Ba wani birnin da ya yi amana da Isra'ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi.
20 Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
21 A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra'ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu.
22 Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu.
23 Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.