2 Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa,
3 daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,
4 da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.
5 Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.
6 Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.
7 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu,
8 da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.