29 Musa kuma ya ba rabin jama'ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu.
30 Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,
31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.
32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun daura da Yariko.
33 Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra'ila, shi ne rabon gādonsu.