3 Gama Musa ya riga ya ba kabilan nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba.
4 Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.
5 Jama'ar Isra'ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri'a.
6 Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.
7 Ina da shekara arba'in sa'ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata.
8 Amma 'yan'uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama'ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci.
9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana ya ce, ‘Hakika duk inda ƙafafunka suka taka a ƙasan nan zai zama gādonka, kai da 'ya'yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahnka sosai!’