2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada,
3 da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem,
4 da Eltola, da Betul, da Horma,
5 da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa,
6 da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
7 Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
8 da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu.