24 Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta.
25 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf,
26 da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat.
27 Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul,
28 da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba.
29 Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib,
30 da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.