1 Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele'azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama'ar Isra'ila.
2 Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan'ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.”
3 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
4 Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.
5 Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.