3 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
4 Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.
5 Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.
6 Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.
7 Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.
8 Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.
9 Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata.