1 Sa'an nan Joshuwa ya kira mutanen kabilar Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa.
2 Ya ce musu, “Kun aikata dukan abin da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku, kun kuma yi biyayya da dukan abin da na umarce ku.
3 Ba ku yar da 'yan'uwanku dukan waɗannan yawan kwanaki, har wa yau ba. Amma kuka kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku sosai.
4 Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun.