1 An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra'ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa.
2 Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,
3 kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.
4 Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.