2 Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.
3 Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan'ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku.
4 Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar.
5 Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.
6 Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku.
7 A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.
8 Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.