1 Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,
2 “Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila.
3 Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.”
4 Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila.
5 Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila.
6 Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?’