13 Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko.
14 A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.
15 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa,
16 “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.”
17 Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun.
18 Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.
19 Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko.