17 Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra'ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra'ilawa.
18 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa
19 'yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta.
20 Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.
21 Sa'ad da Joshuwa da dukan Isra'ilawa suka ga 'yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su.
22 Sauran Isra'ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra'ilawa gaba da baya. Isra'ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere.
23 Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa.