1 Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,
2 sai suka tattaru, suka haɗa kansu domin su yaƙi Joshuwa da Isra'ilawa.
3 Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai,
4 sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki.