3 Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai,
4 sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki.
5 Suka kuma sa tsofaffin takalma waɗanda suka sha gyara, da tsofaffin tufafi. Dukan guzurinsu ya bushe, ya yi fumfuna.
6 Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”
7 Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”
8 Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.”Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?”
9 Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,