11 Manomin da yake aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.
12 Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su sami muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram.
13 Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.
14 Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.
15 Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.
16 Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.
17 Sa'ad da ka faɗi gaskiya, ka yi adalci, amma ƙarairayi su ne jagorar aikata rashin adalci.