16 Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.
17 Sa'ad da ka faɗi gaskiya, ka yi adalci, amma ƙarairayi su ne jagorar aikata rashin adalci.
18 Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
19 Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.
20 Waɗanda suke shawarta mugunta za a auka musu farat ɗaya, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
21 Ba wani mugun abu da zai sami adali, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala.
22 Ubangiji yana ƙin maƙaryata, amma yana murna da masu faɗa da cikawa.