12 Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.
13 Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki.
14 Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin.
15 Firist kuwa zai ɗibi man, ya zuba shi a tafin hannunsa na hagu.
16 Ya kuma tsoma yatsan hannunsa na dama a cikin man da yake a tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa man da yatsansa sau bakwai a gaban Ubangiji.
17 Sauran man da ya ragu a tafin hannunsa, sai ya shafa shi a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da bisa babban yatsan hannunsa na dama, da na ƙafar dama. Wato, za a shafa man a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.
18 Sauran man kuma da ya ragu cikin tafin hannunsa, firist ɗin zai shafa a kan wanda za a tsarkake. Firist zai yi kafara dominsa gaban Ubangiji.