49 Don tsarkakewar gidan, sai maigida ya kawo 'yan tsuntsaye biyu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya.
50 Sai a yanka tsuntsu ɗaya a kasko cike da ruwa mai gudu.
51 Zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai.
52 Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini.
53 Sa'an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka.
54 Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da
55 kuturta a tufafi ko a jikin gida,