52 Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini.
53 Sa'an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka.
54 Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da
55 kuturta a tufafi ko a jikin gida,
56 da kumburi, da ɓamɓaroki, ko tabo,
57 don a tabbatar lokacin da suke tsarkakakku da lokacin da ba su da tsarki.