5 Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai.
6 Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.
7 Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai.
8 Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa'ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden.
9 Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10 Ragowar hadayar garin zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadayar ƙonawa ce mafi tsarki ga Ubangiji.
11 A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.