4 “Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,
5 da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,
6 duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna.
7 To, sa'ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne.
8 Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.
9 “Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka'idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka.
10 “Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake zama tare da su ne, ko kuwa an ɗauke shi yana yi musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.