23 “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
24 sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.
25 Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.
26 Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.
27 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
28 sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.
29 Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.