8 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.
9 Daga cikin hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsensa da wutsiyarsa duka mai kitse. Zai yanke ta gab da ƙashin gadon baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki kuwa, da wanda yake bisansa,
10 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin.
11 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.
12 Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji.
13 Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.
14 Sa'an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,