19 Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta.Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama.
20 Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa.
21 Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.
22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
23 ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya.
24 Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci.
25 Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa.