1 A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,
2 “Da kai da Haruna ku ƙidaya Isra'ilawa, bisa ga kabilansu da iyalansu. Ku tsara sunayen dukan mazaje
3 daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi.
4 Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”