L. Kid 21 HAU

An ci Kan'aniyawa da Yaƙi

1 Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.

2 Sai Isra'ilawa suka yi wa'adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.”

3 Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.

Macijin da aka Yi da Tagulla

4 Isra'ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama'a suka ƙosa da hanyar.

5 Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”

6 Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama'a, suka sassari Isra'ilawa, da yawa kuwa suka mutu.

7 Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.

8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.”

9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.

Tafiya zuwa Kwarin Mowabawa

10 Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya, suka yi zango a Obot.

11 Suka kama hanya daga Obot, suka yi zango a kufafen Abarim a cikin jeji daura da Mowab wajen gabas.

12 Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered.

13 Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda yake cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Gama Arnon shi ne kan iyakar Mowabawa da Amoriyawa.

14 Saboda haka aka faɗa a Littafin Yaƙoƙi na Ubangiji cewa, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na Kogin Arnon,

15 da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”

16 Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, wato rijiya wadda Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane wuri ɗaya, zan kuwa ba su ruwa.”

17 Sai Isra'ilawa suka raira waƙa, suka ce,“Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwaMu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta!

18 Rijiyar da hakimai suka haƙa,Shugabannin jama'a suka haƙa,Da sandan sarauta,Da kuma sandunansu.”Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.

19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.

20 Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.

Mutanen Isra'ila sun Ci Sihon

21 Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,

22 “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”

23 Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa.

24 Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.

25 Isra'ilawa kuwa suka ci dukan waɗannan birane, suka zauna a biranen Amoriyawa, wato a Heshbon da ƙauyukanta duka.

26 Gama Heshbon ita ce birnin Sihon,Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.

27 Domin haka mawaƙa sukan ce,“Ku zo Heshbon, bārin sarki Sihon!Muna so mu ga an sāke gina an kuma fanso shi.

28 Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta,A wannan birni na Heshbon,Sun cinye Ar ta Mowab,Ta murƙushe tuddan Arnon.

29 Kaitonku, ku mutanen Mowab!Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace!Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira,Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.

30 Amma yanzu an hallaka zuriyarsu,Tun daga Heshbon har zuwa Dibon,Har da Nofa kusa da Medeba.”

Isra'ilawa sun Ci Og

31 Haka fa Isra'ilawa suka zauna a ƙasar Amoriyawa.

32 Sai Musa ya aika a leƙo asirin ƙasar Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawan da suke can.

33 Suka juya suka haura ta hanyar Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa suka fita, suka yi yaƙi da su a Edirai.

34 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama'arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.”

35 Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36