L. Kid 16 HAU

Tayarwar Kora, da Datan, da Abiram

1-2 Sai Kora, ɗan Izhara, na kabilar Lawi, iyalin Kohat, ya yi ƙarfin hali ya tayar wa Musa. Waɗansu uku kuma daga kabilar Ra'ubainu suka haɗa kai da shi, su ne Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, da On,ɗan Felet, da waɗansu Isra'ilawa su ɗari biyu da hamsin, sanannun shugabanni da jama'a suka zaɓa.

3 Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama'a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama'ar Ubangiji?”

4 Da Musa ya ji wannan, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu'a.

5 Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.

6 Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare.

7 Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”

8 Musa ya ci gaba da magana da Kora. “Ku Lawiyawa ku kasa kunne!

9 Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra'ila ya keɓe ku daga cikin jama'ar Isra'ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu aiki?

10 Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan 'yan'uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist!

11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”

12 Musa kuwa ya aika a kirawo Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!

13 Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?

14 Banda wannan kuma, ga shi, ba ka kai mu zuwa cikin ƙasa mai yalwar abinci ba, ba ka ba mu gonaki da gonakin inabi domin mu gāda ba, yanzu kuwa kana so ka ruɗe mu, to, ba za mu zo ba sam!”

15 Musa kuwa ya husata ƙawarai da gaske, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace ko jakinsu ba, ban kuwa cuce su ba.”

16 Musa ya ce wa Kora, “Kai da ƙungiyarka duka ku hallara a gaban Ubangiji gobe, da kai, da su, da Haruna.

17 Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”

18 Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.

19 Sai Kora ya tara dukan taron jama'a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama'ar.

20 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna,

21 “Ku ware kanku daga cikin taron jama'ar nan, ni kuwa in hallaka su nan take.”

22 Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”

23 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

24 “Ka faɗa wa jama'a su tashi, su nisanci alfarwar Kora, da ta Datan, da ta Abiram.”

25 Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa.

26 Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

27 Sai jama'a suka tashi daga inda Kora, da Datan, da Abiram suke zama.Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofar alfarwansu tare da matansu da 'ya'yansu, da 'yan ƙananansu.

28 Sai Musa ya ce, “Da haka za ku sani Ubangiji ne ya aiko ni, in yi waɗannan ayyuka, ba da nufin kaina na yi su ba.

29 Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.

30 Amma idan Ubangiji ya aikata wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara zuwa cikin lahira a raye, sa'an nan za ku sani mutanen nan sun raina Ubangiji.”

31 Musa ya rufe bakinsa ke nan, sai wurin da Datan da Abiram suke tsaye, ƙasar ta dāre

32 ta haɗiye su tare da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan mallakarsu.

33 Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai.

34 Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu,kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”

35 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.

36 Ubangiji ya ce wa Musa,

37 “Ka faɗa wa Ele'azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne.

38 Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.”

39 Sai Ele'azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su.

40 Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.

Haruna ya Ceci Jama'a

41 Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”

42 Da taron jama'ar suka haɗa kai gāba da Musa da Haruna, sai suka fuskanci alfarwa ta sujada. Ga girgije yana rufe da alfarwar, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana.

43 Sai Musa da Haruna suka tafi wajen ƙofar alfarwa ta sujada.

44 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa, ya ce,

45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzun nan zan hallaka su.”Sai suka fāɗi rubda ciki.

46 Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki farantin turare, ka cika shi da wuta daga bagade, ka zuba turaren wuta a ciki, ka tafi da sauri wurin taron, ka yi kafara dominsu, gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko, an fara annoba.”

47 Sai Haruna ya ɗauko farantin turaren, ya yi yadda Musa ya ce. Ya sheƙa a guje a tsakiyar taron jama'a. Amma an riga an fara annobar a cikin jama'a. Sai ya zuba turare, ya yi kafara domin jama'a.

48 Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.

49 Waɗanda annoba ta kashe mutum dubu goma sha huɗu ne da ɗari bakwai (14,700), banda waɗanda suka mutu a sanadin Kora.

50 Sai Haruna ya koma wurin Musa a ƙofar alfarwa ta sujada, gama annobar ta ƙare.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36