L. Kid 1:18-50 HAU

18 suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,

19 kamar yadda Ubangiji ya umarta.Musa ya rubuta jama'a a jeji ta Sinai.

20-46 Mazaje masu shekara ashirin ko fi da suka isa yaƙi aka rubuta su suna suna, bisa ga kabilansu da iyalansu, aka fara da kabilar Ra'ubainu, babban ɗan Yakubu. Ga yadda jimillarsu take. Kabila Jimilla Ra'ubainu (46,500) Dubu arba'in da shida da ɗari biyar. Saminu (59,300) Dubu hamsin da tara da ɗari uku. Gad (45,650) Dubu arba'in da biyar da ɗari shida da hamsin. Yahuza (74,600) Dubu saba'in da huɗu da ɗari shida. Issaka (54,400) Dubu hamsin da huɗu da ɗari huɗu. Zabaluna (57,400) Dubu hamsin da bakwai da ɗari huɗu. Ifraimu (40,500) Dubu arba'in da ɗari biyar. Manassa (32,200) Dubu talatin da biyu da ɗari biyu. Biliyaminu (35,400) Dubu talatin da biyar da ɗari huɗu. Dan (62,700) Dubu sittin da biyu da ɗari bakwai. Ashiru (41,500) Dubu arba'in da ɗaya da ɗari biyar. Naftali (53,400) Dubu hamsin da uku da ɗari huɗu. Jimilla duka (603,550) dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin.

47 Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba,

48 gama Ubangiji ya ce wa Musa,

49 “Sa'ad da kake ƙidaya Isra'ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi.

50 A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita.