14 Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.
15 Shugaban rundunar kabilar mutanen Issaka Netanel ne, ɗan Zuwar.
16 Shugaban rundunar kabilar mutanen Zabaluna Eliyab ne, ɗan Helon.
17 Sa'an nan aka kwankwance alfarwar, sai 'ya'yan Gershon, da 'ya'yan Merari masu ɗaukar alfarwar suka kama hanya.
18 Tutar zangon kabilar mutanen Ra'ubainu ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Elizur ne, ɗan Shedeyur.
19 Shugaban rundunar kabilar mutanen Saminu kuwa Shelumiyel ne, ɗan Zurishaddai.
20 Shugaban rundunar kabilar mutanen Gad Eliyasaf ne, ɗan Deyuwel.