33 Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sinai, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki.
34 A duk lokacin da suka tashi daga zango, sai girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.
35 Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.”
36 Sa'ad da akwatin ya sauka kuma, Musa yakan ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubun dubbai na iyalan Isra'ila.”