5 Sa'ad da kuka yi busar faɗakarwa, waɗanda suke zaune a gabashin zangon za su tashi.
6 Sa'ad da kuma kuka yi busar faɗakarwa ta biyu, waɗanda suke a kudancin zangon za su tashi. Sai a yi busar faɗakarwa a kowane lokaci da za su tashi.
7 Amma idan za a kira jama'a ne sai a yi busa da ƙarfi amma banda faɗakarwa.
8 'Ya'yan Haruna, maza, firistoci, su ne za su busa kakakin.“Kakakin za su zama muku ka'ida ta din din din cikin dukan zamananku.
9 Sa'ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku.
10 A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
11 A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada.