2 Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.
3 Aka sa wa wurin suna Tabera, wato matoya, domin wutar Ubangiji ta yi ƙuna a cikinsu.
4 Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra'ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?
5 Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.
6 Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”
7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.
8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.