6 Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”
7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.
8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.
9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.
10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.
11 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?
12 Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’