9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.
10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.
11 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?
12 Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’
13 A ina zan samo nama da zan ba wannan jama'a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’
14 Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina.
15 Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.”