27 Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.
28 Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.
29 Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.
30 Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,
31 gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.
32 Sa'ad da Isra'ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar.
33 Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'a.