39 Sai Ele'azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su.
40 Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.
41 Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”
42 Da taron jama'ar suka haɗa kai gāba da Musa da Haruna, sai suka fuskanci alfarwa ta sujada. Ga girgije yana rufe da alfarwar, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana.
43 Sai Musa da Haruna suka tafi wajen ƙofar alfarwa ta sujada.
44 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa, ya ce,
45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzun nan zan hallaka su.”Sai suka fāɗi rubda ciki.