2 “Wannan ita ce ka'ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra'ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba.
3 Sai ka ba Ele'azara firist ita, sa'an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa.
4 Ele'azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada.
5 Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta.
6 Firist zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar.
7 Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice.
8 Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice.